Da yiwuwar a fara gurfanar da masu sayar da sabbin kuɗi ga ƴan Nijeriya gaban kotu.
Yakamata hukumomin EFCC, ICPC, NFIU su kama tare da gurfanar da mutanen da aka samu suna sayar da sabbin takardun Naira ga ‘yan Najeriya.
Cibiyar dake kiraye-kiraye akan da’ar sarrafa kudaden gwamnati da cigaban al’umma FIDAC, ta shawarci hukumomin EFCC, ICPC, NFIU da sauran hukumomin tsaro su kama tare da gurfanar da mutanen da aka samu suna sayar da sabbin takardun naira ga jama’a, sannan masu POS da aka gano suna karbar sama da Naira 100 kan kowanne Naira dubu 10 na cire sabbin kudi na Naira, a kama su kuma a gurfanar da su a gaban kotu.
Da yake maida martani akan karin wa’adin da babban bankin da shugaban kasa Buhari sukayi, babban daraktan kungiyar ta FIDAC Dr Abdulsalam Muhammad ‘Kani, akwai bukatar babban bankin kasa CBN ya sanya ya zama laifi ga duk wani banki da ya bada tsohon kudi na Naira 200 da Naira 500 da Naira dubu 1 ga abokan cinikinsu daga yanzu kuma duk wani ATM da aka samu ya bada tsaffin kudi a rufe shi sannan a ci tarar bankin.
Yace domin tabbatar da dawowar tsofaffin takardun kudi cikin gaggawa akwai bukatar CBN ya umarci manyan kantunan da gidajen mai da masu POS su karbi tsofaffin takardun kudin daga hannun jama’a sannan a mayar da su bankuna daga bisani.
‘Kani ya kara da cewa domin cike gibin kashi 35.9 na mutane miliyan 38.1 a Najeriya marasa asusun banki kamar yadda wani rahoton kudi na 2020 ya nuna, akwai bukatar babban bankin ya warware matsalolin da suka shafi rashin yawan bankuna da magance rashin aminci tsakanin mutane da bankuna da gyara hanyar sadarwar intanet da wayar da jama’a mazauna karkara da dakile rashin wutar lantarki da rashin samun wutar.
Yayin da yake mika godiya a madadin ‘yan Najeriya ga CBN da fadar shugaban kasa kan yadda suka saurari koke-koke da jama’a sukayi kan bukatar tsawaita wa’adin amfani da kudaden, daraktan FIDAC yace ta dace ayi biyayya tare da la’akari dda tanadin dokar CBN ta 2007 musamman sashe na 20 (3) da (4) da kuma (5) domin guje wa jefa tattalin arzikin Najeriya cikin mawuyacin hali.
Daga Rufa’i Abdurrazak Bello Rogo.