Dakarun Sojojin Nijeriya Sunyi Nasarar Kakkabar Ƴan Ta’adda A Zamfara.
Dakarun Sojojin Nijeriya Sun Yi Nasarar Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama A Jihar zamfara karamar hukumar mulki ta shinkafi Tare Da Kona Mafakar Su.
Labarin dake zo muna a hakin yanzu hakika an samu galaba da nasara akan wadannan yan ta’adda sosai.
Wakilinmu ya samu zantawa da wasu ba’adin Al’umma mazauna yankin sun tabbatar masa cewa! Allah cikin ikonsa ya bawa Sojojin Najeriya din damar ragargazan mafakan yan ta’addan da karkashe wasu ba’adi da daman gaske.
Allah (SWT) ya cigaba da shiga cikin wannan tafiya ya bayar da cikakkiyar nasara da galaba, Allah (SWT) ya zaunar da jihar Zamfara da Nijeriya lafiya alfarmar Annabi Muhammad (SAW).
Allah ka bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali a sassan jahar zamfara da ƙasa baki daya.
RCHP:Belyameen Ahmad Magami.