Dakta Abdullahi Umar Ganduje Ya Mika Mulki Ga Eng. Abba Kabir Yusuf.
Daga Faruq Sani Kudan.
Ganduje ya mika mulki gabanin ranar 29 ga watan Mayu, domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasa.
Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, zai gudanar da aikin mika ayyukan jihar a hukumance ga zababben gwamnan, Engr. Abba Kabir Yusuf, a wannan Lahadi, 28 ga watan Mayu, kwana daya gabanin 29 ga Mayu da wa’adinsa zai cika a hukumance.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida mai barin gado Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana cewa an gabatar da taron ne da misalin karfe 9:00 na daren Lahadi a gidan gwamnati dake Kano.
Ya ce tuni kwamitin mika mulki na jihar Kano ya sanar da kwamitin mika mulki na zababben gwamnan.
Garba ya yi nuni da cewa kwamitocin biyu sun gana ne a cikin makon da ya gabata inda aka gabatar da takardar mika mulki ga kwamitin da aka zaba na gwamna tare da kuma aiwatar da ajandar da ta dace kan bikin mika ragamar mulki.
Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Ganduje zai yi tafiya ne jim kadan bayan taron ya tashi zuwa Abuja a matsayin shugaban tawagar jihar Kano don kaddamar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda aka shirya yi a ranar Litinin, 29 ga Mayu, 2023.
Ya ce ficewar gwamnan ya kuma zama dole don doke wa’adin rufe filin jirgin saman Nnamdi Azikwe Internation Airport, Abuja don bikin rantsar da zababben shugaban kasa.