Dalibin Ogun ya kashe kansa bayan ya rasa kudin makaranta saboda caca
Wani dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Ilaro a Jihar Ogun, Samuel Adekoya ya kashe kansa ta hanyar shan wani sinadari bayan ya rasa kudinsa da na abokinsa a wata caca ta yanar gizo.
Wakilinmu punch ya tattaro cewa marigayin ya yi amfani da kudin makarantarsa wajen yin caca ta yanar gizo a ranar Juma’a amma ya sha kashi.
Adekoya wanda ya kasance dalibin kasa na Diploma II na Injiniyan Lantarki na Lantarki, an ruwaito cewa ya kashe kansa a ranar Litinin, a lokacin da abokan aikinsa ke shirin yin jarrabawar kammala karatunsu na farko.
Rahotanni sun bayyana cewa ya damfari abokin nasa da suke daki da shi ta hanyar samun kalmar sirrin sa sannan ya yi amfani da kudinsa wajen wasa shi ma ya sha kashi.
An tattaro cewa makarantar ta yi gargadin cewa babu wani dalibi da za a bari ya yi jarrabawa ba tare da kammala rajistar sa ba.
An bayyana cewa an garzaya da Adegoke asibitin makarantar inda daga bisani aka mika shi asibitin kwararru da ke wajen makarantar a Ilaro kafin a tabbatar da mutuwarsa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mataimakin magatakardar hulda da jama’a na makarantar, Sola Abiala, ya ce makarantar ta yi gaggawar mika shi asibitin kwararru domin ceto rayuwarsa amma ya mutu jim kadan bayan kwantar da shi a asibitin.
Abiala, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho ya ce “Ya rasu ne a safiyar ranar Litinin a lokacin da ake shirin fara jarabawar.
Ya ce an gano a asibitin kwararru cewa marigayi dalibin ya dauki wani sinadari.
Rahoton Kamal Aliyu Sabongida