Daga Kamal Aliyu Sabongida
Wani da ake zargi da laifin kona ’ya’yansa maza, ya dora alhakin abin da ya aikata a kan “ce-ce-ku-ce” da yakeyi da matarsa.
Joseph Ojo, wanda ‘yan sanda suka kama shi a jihar Ondo ranar Laraba, ya ce matarsa ba ta kula da shi saboda ‘ya’ya biyar da ta haifa a aurenta na baya.
Matar wanda ta kuma haifi ‘ya’ya biyu – tagwaye ‘yan watanni 18 – tare da shi.
Lamarin wanda ya faru a ranar Asabar din da ta gabata a unguwar Fagun Crescent da ke cikin birnin Ondo, ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin yaran.
Daga bisani aka tabbatar da mutuwar biyu daga cikinsu a ranar Talata, sakamakon tsananin konewar da suka samu.
A cewar rundunar ‘yan sandan an fara kai karar ne a sashin Enu-Owa a ranar 5 ga watan Nuwamba.
An ce wani makwabcinsu ya garzaya wurin da lamarin ya faru inda ya yi nasarar ceto hudu daga cikin yaran, yayin da daya ya kone kurmus.
Mahaifiyar yaran ma abin ya shafa yayin da take kokarin ceto ‘ya’yanta.
“An kona Tayo Akinfolarin mai shekaru 7 wanda ba a iya gane shi ba, yayin da sauran yaran hudu aka garzaya da su FMC, Owo.” kamar yanda hukumar ‘yan Sanda suka fitar da sanarwa.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma lura cewa wanda ake zargin ya fusata kan halin matarsa kuma sabida haka dauko mai ya zuba a dakin yaran kafin ya kona su.
“Tagwayen da mahaifiyar yaran ta haifa wa wanda ake zargin suna cikin koshin lafiya, saboda ba su daki daya da ‘yan uwansu,” in ji sanarwar ‘yan sandan.
A cewar rundunar ‘yan sandan, nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.