Fadar shugaban ƙasa a ranar Alhamis ta ce, sanya wa shugaban kasa muhammadu buhari wata hanya a jamhuriyar Nijar alama ce da ke nuna irin mutuntaka da makwabtan Najeriyan ke yi masa.
Babban mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a babban birnin Nijer, Niamey, jim kadan bayan buhari ya kaddamar da wata babbar hanya mai sunan sa.
Shehu ya ce, shugaban jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoun, tare da rakiyar magajin garin Yamai da sauran jami’ai, sun zagaya da Buhari a wani rangadi na babban hanya mai tsawon kilomita 3.8 wanda aka kaddamar da shi bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar.
Hadimin shugaban ƙasar ya ruwaito cewa Buhari yana bayyana gamsuwa da alaƙar da ke tsakanin Najeriya da makwabtanta.
Buhari ya bayyana imanin cewa irin wannan alaƙar ta taimaka matuƙa, musamman a fannin magance matsalar tsaro a kan iyakokin jasar, da shigo da makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma fasa kwauri.
Shehu ya ce Buhari ya hau karagar mulki a shekarar 2015, ya bude wata tattaunawa mai karfi da kasashen Nijar, Benin, Chadi, da Kamaru, lamarin da ya haifar da kyakkyawar alaka ta diflomasiya da ke da moriyar juna ga kasashen biyu.
“Shugaba Buhari yana matukar mutunta makwabtanmu, kuma ya fahimci ma’anar kyakkyawar makwabtaka.
“Kafin wannan gwamnatin, wasu daga cikin wadannan kasashe sun yi korafin cewa shugabannin Najeriya ba suyin magana da su, Amma mu mun bude tattaunawa da su kuma bukatu yana biya.
Shehu ya kara da cewa, “muna hada kai da su kan muhimman al’amura, musamman a fannin tsaro, magance fasa-kwauri, da shigo da muggan makamai, don haka hadin gwiwar ya kammala.”
Mai taimaka wa shugaban kasa ya yi imanin cewa bubari zai bar baya a ranar 29 ga Mayu, 2023, kyakkyawar dangantaka, wadda aka gina a kan tsayayyen dutse tare da makwabtan Najeriya kuma ana sa ran magajinsa zai gina shi.
Shugaban na Najeriya ya ziyarci kasar Niamey ne domin halartar taron kungiyar tarayyar Afirka (AU) kan bunkasa masana’antu da habaka tattalin arziki.
Labari: Kamal Aliyu Sabongida.