Dalilin da yasa kyawawan mata suke shan wahala wajen samun mijin aure.
Za’a iya cewa, kusan duk matan da Allah ya jarrabesu da kyau irin tasu kalan jarabawan kenan wanda ba kowace kyakkyawa bane take iya cinye wannan jarabawa.
Kowace mace tanada jerin ra’ayoyin na tunanin halayen da take nema wajen zaben mijin aure.
Mafi yawan mata masu kyau jerin ra’ayoyinsu yafi tsayi fiye da na namiji saboda haka sunada ka’idoji akan irin mutanen da zasu iya tarayya dasu ko akasin haka.
_suna sane suke watsar da samarin da suke nemansu da aure.
Wannan dalili ya kunshi duk dalilan da kesa mata masu kyau wahalan samun mijin aure saboda sunada kawa zuci fiye da kowace mace.
_Basu shakkan kansu duk dadewan da zasuyi basu aure ba.
_Da yawansu basu neman sulhu a gurin samarinsu idan sun sami savani.
_Basu kula saurayin da bashi kyau sunfi zaben saurayi mai kyau fiya da cancanta.
_suke tsara ma kansu lokacin da zasuyi aure.
_Basu damu da zama su kadai ba.
_mafiya yawansu sun dogara da kansu ne.
_sunada fahimtan abinda suke so matuka.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.