Dalilin Da Yasa Muke So A Binciki Shugaban Hukumar EFCC – Matasan Neja-Delta
…. Matasan yankin Neja Delta sun buƙaci shugaban hukumar EFCC da ya ajiye shugabancin hukumar da yake, domin ya bawa masu bincike damar gudanar da zuzzurfan bincike akan abinda ake tuhumarsa
Matasan yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur, kungiyar matasan Neja Delta (NDYC) sun bayyana matukar damuwarsu game da jerin zarge-zargen da ake yi wa Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mista Abdulrasheed Bawa.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetan hukumar ta NDYC, Kwamared Israel Uwejeyan, matasan sun ci gaba da cewa, “wadannan zarge-zarge, idan har sun tabbata, suna da yuwuwar kawo cikas ga sahihanci da ingancin hukumar. Saboda haka yana da muhimmanci a gudanar da cikakken bincike kan wadannan zarge-zargen”, in ji sanarwar.
A bisa wadannan manyan zarge-zarge, muna kira ga majalisar dattawa da ta gudanar da cikakken bincike a kan lamarin don tabbatar da gaskiya, rikon amana, da kuma kiyaye mutuncin EFCC. A matsayinmu na masu kula da dimokuradiyyar mu, majalisar dattawa tana da hurumin yanke hukunci mai mahimmanci da ke da tasiri kai tsaye ga jin dadi da makomar kasarmu musamman yadda ta shafi manyan cibiyoyi irin su EFCC.
Dole ne mu yi aiki tare don tabbatar da cewa EFCC ta ci gaba da kasancewa cibiya mai inganci ta yaki da cin hanci da rashawa, tare da kiyaye ka’idoji na adalci da rikon amana.