Da Tsarin Allah,Da Tsarin Democoraɗiya Wanne Ne Yafi Zama Dai-Dai Da Mu Musulmi?
Malamin mazaunin katsina mai suna Shaikh yakubu Yahaya, yayi jan kunne ga masu ganin cewa aci gaba da damawa a tsarin demokoradiya,
Malamin yace “Yanzu mu dawo a ilmance a addininance, aka ce “Wala Yaf’alu fi’ilan hatta ya’alamu hukumullahu fihi” ma’ana (kada ka aikata aiki sai ka san hukuncin Allah a cikinsa) To a matsayinka na wanda kayi Imani da Allah da Manzonsa da Littafinsa, Minene hukuncin yin aiki da wani abin da ya saɓa ma littafin da Allah ya aiko Manzonsa da shi?.
Shehin malamin ya cigaba da cewa, ƙaddara duk mun rungumi dumukuraɗiyya muna yi, kuma mun yarda ita ce mafita. Shin minene ladar yin dumukuraɗiyya da bin wannnan tsarin da ya saɓa ma na Allah?
Ban ce maka ga wanda basu da addini ba a’a ga masu addini nake magana, mu da muke da makoma da wuta da aljanna, muke son muje mu shiga aljanna da rahmar Allah. To da tsarin nan na Allah da muke magana a kansa da tsarin dumukuraɗiyya wanne ne yafi zama da-dai da mu Musulmi? Nasan zaka ce tsarin Allah ne dai-dai, to mi yasa muke yin wannan?
To mu ƙaddara darajarsu ɗaya. Da tsarin Allah da na dumukuraɗɗiyya, wane ya kamata mu zaɓa? Shima ƙila kace na Allah, to mi yasa muka barshi muka zaɓi wancan?
Sannan duka-duka shekara nawa kenan aka fara dumukuraɗiyya ba 20 kenan ba? (1999 ne ai zuwa yanzu). To daga wancan lokacin zuwa yanzu a dumukuraɗiyyance ina muke dosa? Tambayi kowwa, gaskiyar magana bamu san ina muke sa gaba ba, to idan bamu san ina muke sa gaba ba tun daga 1999 tenuwa ta 1 aka yi ta 2 aka ƙara, har yau gashi nan za’a shiga wata tenuwar. Yanzu in daga can sadda muka taso (1999) muna cikin duhu ne yanzu kuna son mu dasa cikin wani sabon duhun ne mu ƙara gaba?
Tayiwu wani yace; kai dai duk kewaye-kewayenka so kake a dawo kan tsarin addini. To tambaya, shin addinin bai dace ba? bai kamata ayi shi ba? Allah bai so? Annabi bai so ayi? A matsayinka na mai addini (Musulunci nake maka wannan maganar ka rabu da waɗanda basu da shi) Nan ma ƙila kace ya dace ayi, to yaushe za a yi?
Ta yiwu kace ai ƙasar ce kamar ba zai yiwu ba ga kiristoci, ga kaza ga kaza. Sai muce maka addinin kayan waye? (Allah) to mu fuskance shi mu ga idan bai taimaka mana ba”.
Mujahid Umar D Giwa.