Dan Sanda Ya Mutu Bayan Harin Da Wasu Mutanen Kauyen Neja Suka Kai Musu
Yanzu haka dai wasu mutane biyu da ake zargi suna hannun ‘yan sanda a jihar Neja bisa zargin kashe wani dan sanda mai suna Nasiru Yusuf.
An kama su ne a kauyen Minima da ke karamar hukumar Lavun a jihar kan zargin kisan kai.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Minna, babban birnin jihar a ranar Lahadin da ta gabata cewa, kisan ya faru ne a lokacin da wasu mahara suka kai hari kan wasu ‘yan sanda guda biyu da ke bakin aiki a yankin.
Abiodun ya ce, “Akwai korafin cin zarafi da tada kayar-baya a yankin kuma an yi wa ‘yan sanda biyu cikakken bayani a wurin da lamarin ya faru a kauyen Minima domin gudanar da bincike tare da kama su.
“A cikin haka ne mutanen kauyen suka far wa ‘yan sandan biyu, inda suka yi musu rauni.
“An kai su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Bida domin yi musu magani, daga baya kuma an tabbatar da mutuwar daya daga cikinsu PC Nasiru Yusuf a asibiti yayin da dayan ke ci gaba da samun kulawa.
“An kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a cikin lamarin, kuma ana ci gaba da yi musu tambayoyi, saboda ana gudanar da bincike kan lamarin.”
Abiodun ya kara da cewa za a gurfanar da mutanen biyu zuwa kotu bayan an kammala bincike.
Rahoto Abdulnasir Yusuf (Sarki Dan Hausa)