Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar LP ya koma APC.
Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar Labour party, Bashir Bashir, a yammacin Lahadi ya fice daga jam’iyyarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Bashir, tare da jiga-jigan jam’iyyar LP a Kano, a ranar 21 ga watan Janairu, ya ki amincewa da taron gangamin jam’iyyar da aka gudanar a Kano.
Sauran ‘yan jam’iyyar LP da suka kaurace wa taron su ne Mohammed Zarewa; kodinetan yakin neman zaben Peter Obi na jihar, Balarabe Wakili; da kuma dan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Idris Dambazau.
Wata majiya da ke kusa da Bashir ta tabbatar da sauya shekarsa da wasu shugabannin LP na Kano zuwa APC a ranar Lahadi ga wakilinmu.
Majiyar ta kuma alakanta matakin nasa da yadda jam’iyyar ta kebe manyan masu ruwa da tsaki a yankin Arewa wajen yanke hukunci, da kuma rashin fitar da sahihin alkibla kan muradun arewacin Najeriya.
A halin da ake ciki dai yanzu Jam’iyyar ta Labour party ba tada ɗan takara a jihar ta Kano.