Dan wasa Jao Cancelo yace komawa Manchester City da yayi shine abu mafi kyawu a rayuwar sa ta kwallon kafa.
alfijirhausa.com ta rahoto.
Dan wasan bayan gefen damar na kasar Portugal yana samun kira na komawa Real Madrid a wannan kakar.
Kamar yadda ya fada a shafin Man City yau: “Eh tabbas bani da tantama akan hakan. Komawa Manchester City da nayi shine abu mafi kyawu a rayuwata ta kwallon kafa.
“Tabbas nayi wasa a manyan kungiyoyi a nahiyar turai kamar su Benfica, Valencia, Inter Milan, Juventus, Amma ina tunanin komawa Manchester City yasha bamban da sauran wadancan matakan.
“Wata shidan farko da nayi basu zo da kyau ba. Ina bukatar lokaci kafin na kama. Amma yanzu komai yayi daidai.
“Ina fatan zan sake shafe tsawon wasu shekarun a Man City saboda inajin dadi. ”