Dangote ya godewa Mahukunta Najeriya da yan Najeriya na Ganin kammaluwar Matatan Mansa.
Muna Godiya ta Irin Goyon Bayan Da Kuka Wajen Kafuwar Wannan Muhimmin Aiki – Dangote ga ‘yan Najeriya.
Babban Jami’in Kamfanin Dangote Industries Limited, Aliko Dangote, ya jinjinawa Shugaban Kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), da zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu, da ‘yan Nijeriya baki daya bisa goyon bayan da aka bayar wajen kafa matatar man fetur ta Dangote Petrochemicals.
Dan kasuwar ya bayyana jin dadin sa ta shafin Twitter na kungiyar a ranar Litinin.
Rahoton PUNCH ta rahoton matatar da aka kafa don tace ganga 650,000 na danyen mai a kowace rana na canza danyen mai zuwa samfuran mai daban-daban kamar dizal, man fetur, man jiragen sama da kananzir.
Matatar za ta samar da man fetur da dizal mai inganci na Euro-V, da man jet da kuma polypropylene.
Kamfanin ya bayyana cewa an tsara ginin ne domin sarrafa danyen mai iri-iri, da suka hada da danyen mai da yawa na Afirka, wasu danyen mai na Gabas ta Tsakiya, da kuma Man Fetur na Amurka.
“To, abin da nake so in raba wa ’yan Najeriya shi ne don in nuna godiyata bisa taimakon da muka samu daga Shugaban kasa, daga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, har ma da Shugaban Kasa mai jiran gado, domin ya kuma kafa hanyar samar da yankin ciniki cikin ‘yanci na Lekki a matsayin wani bangare na mafarkinsa.
“Haka zalika muna son mika godiya ta musamman ga Gwamna Fashola da Gwamna Ambode da musamman Gwamna Sanwo-Olu; domin sun ba mu dukkan taimakon da muke nema.
“Muna godiya ga dukkan ‘yan Najeriya da suka ba mu goyon bayan mai tarin yawa,” in ji Dangote.
Tun da farko dai jaridar PUNCH ta ruwaito zuwan shugaba Buhari.
Buhari ya samu tarba daga gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida