Dauda Lawal Ya Nemi Karin Tallafin Sojoji A Zamfara.
Gwamnan Zamfara, Lawal, Ya Nemi Karin Tallafin Sojoji Domin Shawo Kan Matsalar Tsaro Da Ke Addabar Jahar.
Gwamnan Jahar Zamfara, Dauda Lawal, ya nemi karin tallafin sojoji domin shawo kan kalubalen tsaro da ke addabar jahar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya kara da cewa Lawal yana hedikwatar tsaro da ke Abuja, inda ya ke tattauna da babban hafsan sojin ‘kasar, Janar Lucky Irabor.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa a wani bangare na kokarin Gwamna Lawal na wanzar da zaman lafiya da tsaro a jahar Zamfara, ya gana da hukumar CDS domin tattaunawa kan muhimman batutuwan tsaro da tsare-tsare na nan gaba.
Kudirin gwamnatin jahar Zamfara ne ta amince da alhakin da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya na samar da tsaro a cikin gida wanda ya hada da hada kai da sojoji.
Gwamnan ya damu da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan jahar Zamfara, wanda ya zama dole a hada kai da duk hukumomin tsaro da abin ya shafa domin a samu zaman lafiya a jahar,” inji Idris.