Dilallan Man Fetur Sun Gana Da Shugaban Kasa Bola Tunubu.
Shugaba Bola Tinubu ya umurci Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da ta yi amfani da hanyar da za ta fara aiki da shisshigi don rage tasirin cire tallafin ga ‘yan Najeriya.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ne ya bayyana haka bayan ya jagoranci wasu manyan ‘yan kasuwar man fetur a ziyarar ban girma da suka kai wa shugaban kasar a fadar gwamnati da ke Abuja.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, Abiodun, wanda tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ne, ya bayyana cewa ‘yan kasuwar sun nuna goyon bayansu ga shugaban kasa kan cire kudin tallafin N4trn, matakin da zai iya karawa kwamitin da ke kula da asusun ajiyar kudi na tarayya FAAC kudaden Shíga.
Daga baya kungiyar ‘yan kasuwan sun bayyana aniyarsu ta bayar da gudumawar bas din motocin jigilar mutane 50 zuwa 100, masu dauke da mutane hamsin wadanda za su rika tafiya a kan CNG, inda za su ci N100m kowanne da N10bn, domin rage tasirin cirewar cikin kwanaki 30 masu zuwa.