Duk matan da zan aura saita koyi dafa abincin da nakeci agun mamana na wata hudu_inji wani matashi.
Wani matashi mai suna Mazil Ifeanyi ya bayyana ma duniya cewa, duk matan da zai aura saitaje gidnasu ta zauna da mahaifiyanshi tsawon wata 4 ta koyi abubuwan da akeyi mishi.
Yace, inada zabi game da nau’in abincin da nake ci.
Don haka duk matan da zan aura saita fara zuwa tayi zaman watanni 4 da mahaifiya ta ko kanwata don ta koyi yadda suke yimin girki da abubuwan da nakeson a girkamin.
Yace, komin son da nake yima budurwa indai bazataje wajen mahaifiyata ta koyi girki ba to bazan aureta ba inji shi.
Shiyasa aure a shekarun baya yafi dadi da tasiri domin matan wancan lokacin duk abinda kake so zasuyi maka.
suna daukan mijinsu tamkar wani sarki sabanin matan yanzu, cewan matashin.
Inda yace, inada kudi inada duk abinda ake nema agun namiji idan akwai wadda taga zata daukeni a matayin miji kuma sarki toh ina jira daga gareta.
Matashin ya bayyana hakane a shafinshi na tiwita.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.