Nan bada dadewa ba gaba daya duniya zata zama kasan musulunci-babban pasto na kasan Rasha.
A cewan shugaban cocin Rasha, kasashen turai irin su kasan Rasha da sauran kasashen yammacin Turai duk sun fara zama ƙasan musulunci saboda a kasan jamus kashi 30% cikin dari na kiristocin kasan duk tsofaffi ne, hakan yasa kashi 70% na matasa masu jini a jika na jama’an kasan zasu zama musulmi nan ba da dadewa ba.
Paston yaci gaba da cewa, a kasan shi ta Rasha kiristoci suna cika filayen kwallo, da gidajen Rawa Disco, amma a ranakun ladi saikaga babu kowa a coci, amma a gefe daya musulmi suna cika masallatai don gudanar da ibada.
Abin mamaki ne yadda dubban musulmi sukeyin dandazo a manyan filaye wasanni don gudanar da sallolin idi, wannan ba karamin abun mamaki bane.
Sannan duk inda kashiga a ingila zakaji anata ambaton sunan Annabi Muhammad (S A W).
Sannan a halin yanzu kaso 49% na mazauna birnin Brussels, duk musulmi ne don haka nake kara jaddadawa nan bada jimawa ba duk duniya zata zama kasan musukunci inji shi.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.