EFCC ta roki Babban Kotun kasa cewa kada a saki Manyan Kadarori 14 na Yahaya Bello.
Hukumar EFCC ta roƙi Babbar Kotun Tarayya cewa kada ta bada umarnin a saki manyan kadarori 14 da hukumar ta riƙe, waɗanda ta ce ta haƙƙaƙe da kuɗaɗen al’ummar Jihar Kogi ne Gwamna Yahaya Bello ya saye su.
Su kuma jibga-jibgan lauyoyin da Yahaya Bello ya ɗauka, sun ce umarnin ƙwace gidajen da kotu ta bai wa EFCC, ya keta ‘yancin da doka ta bai wa Gwamna Bello, a matsayin sa wanda Kundin Tsarin Mulki ya ba shi kariyar kamawa ko gurfanarwa kotu.
Wannan jarida ta bada labarin yadda a ranar 22 ga Fabrairu, Mai Shari’a Nicholas Oweibo ya bayar yanke hukunci cewa EFCC ta ƙwace maka-makan gidajen 14, tare da wasu kuɗaɗe naira miliyan 400.
Kadarorin 14 dai an gano su ne a Legas, Abuja da kuma Dubai.
EFCC ta ce binciken da ta yi ya nuna mata cewa kuɗaɗen da aka sayi kadarorin daga hannun Yahaya Bello, ko kuma shi aka yi wa dillancin sayen gidajen, kuma aka biya a madadin sa.
A ci gaba da sauraren shari’a ranar Talata, lauyan EFCC Rotimi Oyedepo wanda babban lauya ne, wato SAN, ya ce bai ga dalilin da lauyan Yahaya Bello mai suna Abdulwahab Mohammed zai zo kotu ya nemi a soke umarnin riƙe gidajen da kuɗaɗen ba.
Shi lauyan Bello cewa ya yi gwamnan ya sayi yawancin gidajen ne tun kafin ya zama Gwamnan Jihar Kogi.
Don haka ya ce kotu ba ta ƙarfin ikon ƙwacewa ko gurfanar da Yahaya Bello, domin ya na sanye da rigar kariyar haramta maka shi kotu ko kama shi.
Sai dai lauyan EFCC ya ce hukumar ta bayyana wa kotu yadda aka sayi gidajen, kuma Bello da lauyoyin sa sun kasa ƙalubalantar bayanin da EFCC ta yi wa kotu na yadda aka sayi gidajen.
Mai Shari’a ya ɗage zaman tankiyar zuwa ranar 20 Ga Afrilu, domin ya duba yiwuwa ko rashin yiwuwar sakin kadarorin.