Furucin Aminu Sani Jaji Na Cewa Shine Silar Nasarar Bola Tunubu Ya Tada Kura.
Kungiyoyin Magoya Bayan Tinubu Na Arewa Maso -Yamma Sun Musanta Iƙrarin Aminu Sani jaji.
Gamayyar kungiyoyin sun ƙaryata kalaman da Aminu Sani Jaji yayi na cewa shine silar nasarar zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya Alh Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023 a Arewa maso-yamma.
Yayin taron manema labarai daya gudana a gamayyar su ka yi a jihar Kaduna a yau Talata 16/05/2023 sun nesanta kansu kuma sun yi kakkausar suka ga ikirarin na wani da ake kira da Aminu Sani Jaji bisa nasarar shugaban kasar Najeriya na jam’iyyar APC a zaɓen da ya gudana.
A cikin rahotan da suka karantawa manema labarai yayin zaman sun jaddada cewa ko kusa su basu san wata gudunmawar da Aminu Sani Jaji ya bayar ba, domin kuwa sune suke Arewa maso-yamma kuma su ne suka shiga suka fita wajen tabbatar da wannan nasarar.
Mai magana da yawun gamayyar ya bayyanawa manema labarai cewa gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawallen Maradun shine mutum ɗaya tilo da yayi ɗawainiya da su wajen tabbatar da wannan nasarar, saboda shine ya shiga ya fita wajen ganin wannan tafiya a Arewa maso-yamma ta cimma gacin da ake buƙata.
Matawalle shine mutum ɗaya tilo da ya shiga wannan hidimar da lokacinsa da kuma dukiyarsa, ya kuma tallafawa wannan gamayyar bugu da ƙari ya shiga wajen ganin ya samu nasarar neman goyan bayan dattijan yankin da kuma manyan Malaman yankin na Arewa maso-yamma.
Bisa wannan dalilai ita wannan gamayyar wacce take ɗauke da kungiyoyi sama da hamsin (50) a ƙarkashin ta haɗu a jihar Kaduna domin nisanta kanta da kuma ƙaryata wancan iƙrarin na shi wancan mutumin Aminu Sani Jaji, domin babu wata gudunmawa da ya bawa zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya Alh Asiwaju Bola Ahmed Tinubu don tabbatar da nasarar sa a kakar zaɓen da ya gudana.
Kungiyoyin sun gudanar da taron na manema labarai tare da wakilcin dukkan kungiyoyin da suka marawa zaɓaɓɓen shugaban kasar baya da suke shiyyar Arewa maso-yamma.