Saura Watanni Uku 3 Ayi Zabe, Shugaban INEC Ya Bayyana Babban Abin Da Yake Damunsa.
Shugaban hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya ya yi wani jawabi a makarantar NIPPS.
Farfesa Mahmood Yakubu ya damu kan yadda ‘yan siyasa suka bijiro da dabarun sayen kuri’un zabe.
Yakubu yace duk gyare-gyaren da ake yi wa dokar zabe, ‘yan siyasa na fito da miyagun dabarunsu.
Shugaban hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta watau INEC, Mahmood Yakubu ya koka a kan irin yadda ake sayen kuri’u.
A rahoton da muka samu daga Vanguarda ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba 2022, Farfesa Mahmood Yakubu ya nuna sayen kuri’u ya fara yawa.
Shugaban na INEC ya kuma fadi cewa kayan da ake amfani da su wajen gudanar da zabe suna cikin barazana saboda rashin tsaro da ake fama da shi.
Idan aka tafi a haka, Mahmood Yakubu yana ganin cewa INEC za ta fuskanci matsaloli a 2023.
Rahoton yake cewa Farfesa Mahmood Yakubu ya yi wadannan koke-koke ne da ya gabatar da jawabi a wajen wani taro da aka shirya a cibiyar NIPPIS.
Masu ruwa da tsaki da jam’iyyun siyasa sun shirya wannan taro kamar yadda aka saba duk shekara domin ganin yadda za ayi zabe na gaskiya.
Hauwa Habib wanda Darekta ce a INEC, ta wakilci shugaban hukumar a wajen taron da aka yi.
A jawabinsa, shugaban INEC ya yi kira ga jam’iyyun siyasar kasar nan da su ilmantar da ‘ya ‘yansu kan abubuwan da suka dace da wadanda ba su dace ba.
Yakubu yake cewa tun daga 1999, kullum ana gyara dokar zabe ne, amma kuma ba za ta yiwu a aiwatar da dokar ba tare da hadin-kan jam’iyyun siyasa ba.
Saboda haka ne aka yi wa dokar zaben 2010 kwaskwarima 83 a sabuwar dokar zaben 2022 da aka shigo da ita, wanda za ta fara aiki a zaben shekarar badi.
A game da sayen kuri’u, INEC tace abin ya kai tun jam’iyyu na fada da junansu, yanzu ta kai suna kokarin kawo tasgaro wajen kokarin da hukuma take yi.
Habiba tace da zarar hukumar INEC ta kawo doka, sai ‘yan siyasa su fito da sabuwar dabarar da za su rika bi domin su biya kudi wajen kuri’un mutane.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.