Gardawan Da Suka Aukawa Yar Shekara 15 A Neja Sun Shiga Hannu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama Nuhu Mohammed mai shekaru 26 da Sani Usman mai shekara 22 mazauna garin Izom dake karamar hukumar Gurara bisa laifin kashe ‘yar shekara 14 Ubaida Surajo.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Wasiu Abiodun ya bayyana cewa mutanen sun kashe Ubaida a gidan Iyayen ta a ranar 5 ga Yuni a lokacin da mahaifiyar ta bata gida ta tafi kasuwa.
Abiodun ya ce da ya shiga hannun jami’an tsaro Mohammed ya ce suna zama a gida tare da mahaifiyar Ubaida yana mai cewa ya kashe Ubaida saboda wai wata rana mahaifiyar yarinyar ta zarge shi da yi mata sata har Naira 90,000.
“Ya ce ya kira abokinsa Usman inda suka zauna suka jira har sai lokacin da Ubaida ta dawo gida sannan suka kashe ta.
“Mohammed ya ce bayan sun kashe yarinyar sai suka kulle kofar shiga gidan sannan suka gudu.
Abiodun ya ce wukake guda shida, adduna biyu, diga daya da riga da jini na daga abubuwan da jami’an tsaro suka kama a dakin Mohammed.
Bayan haka rundunar ta kama Mohammed Bande wanda aka fi sani da Kachallsa mazaunin.
Abiodun ya ce ‘yan sanda sun samu naira miliyan 1.7 a dakin Bande sannan ko da ya shiga hannun jami’an tsaro Bande ya ce wani Gora ya bashi kudin domin ya siyo masa makamai.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.