Gaskiyar Abinda Aka Tattauna Tsakanin Tinubu Da Sunusi.
Nazo in godema Tinubu akan matakan da ya dauka wajen dawo da tattalin Arzikin kasa.
Tsohon Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan Bankin Nigeria CBN Sarkin Sanusi || ya gana da Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmed Tinubu yayin ganarwa tasu Sarki Sanusi ya mika sakon barka da taya Shugaban murna zama Shugaban Kasar tare da fatan sauke nauyin da ke kansa.
Yayin ganawarsu tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi yace yazo nan ne domin gode ma Shugaban kasa akan matakan da ya dauka wajen dawo da Tattalin Arziki akan hanya. Ya kara da cewa idan yan kasa suka yi hakuri tabbas za a samu inganci a cikin wannan tsari da Shugaban kasa ya dauka.
Jiya Alhamis da yamma ne tsohon Sarkin Kano ya samu damar ganawa da shugaban kasar.