Gwamna El-rufa’i Ya Cigaba Da Rùsa Muhallan Mabiya Mazhabin Shi’a A Garin Kaduna.
Mun samu Rahoton dake Tabbatar Mana da cewa; Gwamna Mai shirin barin gado na jihar Kaduna Maigirma Mal. Ahmad El-rufa’i ya ci gaba da rùshé Wasu Muhimman Muhallai Na Mabiya Mazhabin Shì’à dake Garin Kaduna.
Wasu daga cikin Guraran da Gwamnatin Kaduna Tasa aka Rusa na Harka islamiya karkashin Jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky a cikin Garin kaduna a cikin wannan daran na Asabar.
Gwamnatin Ta Rusa Guraran da Yan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky suke gudanar da karatuttukansu tare da Tsarukansu na Musulunci, sannan suka Rushe Asibitin da ake Kira da Alkhausar dake hayin Rigasa.
Rahotonnin sun ci gaba da zuwa Mana cewa; Gwamnatin Jihar Kàdunà ta rusa Makarantu biyu rigis duk da suke Rimi, Rigasa ɗan Madami duk a cikin rigasa.
Sun Rusa Gaban Gidan Malam Musa Birnin yaro dake kawo cikin dare nan, sannan a cikin daren.