“Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da umarnin daukar likitoci a jahar.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da umarnin daukar likitoci, ma’aikatan jinya da sauran kwararrun kiwon lafiya wadanda ‘yan asalin yankin Shani ne domin magance matsalar karancin ma’aikata a cibiyoyin kiwon lafiya na karamar hukumar.
Zulum ya bayar da umarnin ne a fadar mai martaba Sarkin Shani, Alhaji Muhammadu Nasiru Mailafiya yayin da ya gabatar da jawabi a ranar Lahadi.
“Ya kamata shugaban karamar hukumar ya tattara tare da mika sunayen ’yan asalin Shani da suka yi karatun likitanci da aikin jinya da sauran sana’o’in da suka shafi kiwon lafiya domin a yi musu aiki don cike gibin da ake samu na ma’aikata.
“Idan ba za ku iya isa ba, ina ganin a matsayin mafita na dogon lokaci, za mu iya daukar nauyin yara kanana don yin karatun likitanci da sauran darussan kiwon lafiya, domin su dawo gida su cike gibin,” in ji Zulum.
Amincewar ranar Lahadi na daya daga cikin da yawa da gwamnatin Zulum ta yi da nufin samar da ayyuka masu araha da inganci ga al’ummomin karkara a fadin jihar.
Wasu jerin amincewar da Zulum ya yi sun hada da daukar ma’aikatan lafiya 594, daga cikinsu, likitoci 86, ma’aikatan jinya 365 da ungozoma, masu harhada magunguna 45 da ma’aikatan lafiya 100 da sauran ma’aikatan tallafi a watan Satumbar 2020.
An kuma amince da karin likitoci 40 a cikin Janairu 2021 don biyan bukatun kiwon lafiya na karuwar yawan jama’ar Borno.
Na baya-bayan nan dai shi ne daukar ma’aikatan lafiya 30, ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya a watan Satumba, 2022 zuwa babban asibitin Bama da mayakan Boko Haram suka lalata.
Tun a shekarar 2019 Zulum ya gina cibiyoyin kiwon lafiya da dama tare da inganta wadanda suke da su, wasu daga cikinsu mayakan Boko Haram sun lalata su.
Bisa kididdigar da bankin duniya ya yi na farfadowa da samar da zaman lafiya, an lalata cibiyoyin kiwon lafiya 201 sakamakon tashe tashen hankula da aka kwashe shekaru goma ana yi.
RAHOTO -ALIYU SHU’AIBU ALIYU (MARIRI)