Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya gayyaci dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP Engr Rabi’u Musa Kwankwaso don bude wasu aiyuka da gwamnan yayi a jihar ta shi.
Yayin kaddamar da aiyukan dan takarar shugaban kasar ya jaddadawa Wike cewa ita kwankwasiyya ba dole sai ya saka jar hula ba, don haka shima wike ɗin ɗan Kwankwasiyya ne a yanzu da kuma kowanne lokaci a nan gaba, inji Kwankwason.
A nashi bangaren kamar yadda jaridar Channel Television suka wallafa gwamnan ya nuna yabawa tare da jajircewa irin ta kwankwaso, haka-zalika ya bayyana cewa zai taimakawa dan takarar kuma ya dafa masa musamman a jiharsa ta Rivers a 2023.
Shin ko hakan na nufin Nyeson Wike zai yi anty-party ne ko kuma zai taimakawa dan takarar ne wajen cimma burikansa a nan gaba, wannan kuma lokacine alƙali.
Daga Comrd Hasheem Haidar Kano.