Gwamnatin Katsina Ta Kwace Filayen Da Aka Rabawa Wa Mutane
Gwamnan Ƙatsina, Malam Dikko Radda, ya soke filayen da wasu jami’an gwamnati suka raba wa mutane
A wata sanarwa daga ofishin shugaban ma’aikata, sabon gwamnan Katsina ya ce ba’a bi doka wajen raba filayen ba
Dikko Radda na jam’iyyar APC ya gaji tsohon gwamna Aminu Bello Masari, wanda jam’iyyarsu daya
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya soke filayen da tsohuwar gwamnati karkashin Aminu Bello Masari ta raba wa mutane a fadin jihar.
Leadership ta rahoto cewa wannan mataki na kunshe a wata sanarwa da daraktan sashin albarkatun kasa na ofishin shugaban ma’aikatan Katsina, Ado Yahaya, ya fitar.
Ya ce gwamna ya nuna takaicinsa da rashin jin dadi kan yadda wasu shugabannin ma’aikatu a jihar suka raba filayen ba ta hanyar da doka ta tanada ba.
A cewar Malam Radda, ya zama tilas ya dakatar da lamarin domin gwamnatin jiha ta hannun ma’aikatar kula da filayen kasa ne kadai ke da hakkin mallaka wa wani filo komi kankantarsa.
“Bugu da kari, duk wasu filaye da aka mallaka wa mutane ba tare da bin ka’idoji da tanadin doka ba, an soke su daga yanzu.”
“Haka nan kuma duk wani jami’in gwamnati da aka gano da hannunsa a rabon wadannan filaye ba bisa ka’ida ba zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata na saba doka,” inji shi.
Gwamna Malam Dikko ya dauki wannan mataki ne kusan makonni biyu bayan ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin zababben gwamnan Katsina ranar 29 ga watan Mayu.
Radda, wanda ya lashe zaben 18 ga watan Maris, da kuri’u masu rinjaye ya gaji tsohon gwamna, Aminu Bello Masari, na jam’iyyar APC mai mulki.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim