Gwamnatin Tarayya Da Ta Ogun Sun Fara Yi Wa Dabbobi Allurar Riga-Kafin Cututtuka
A bisa kokarin rage yaduwar cutukan da ke harbin dabbobi zuwa cikin alumma, gwamnatin tarayya da jihar Ogun sun fara yiwa dabbobi Allurar rigakafi a jihar ta Ogun.
An fara yin aikin ne, bisa hadaka a tsakanin ma’aikatar aikin noma da raya karkara da gwamnatin jihar bisa taimakawar shirin yakar cutukan dabbobi na shiyya RDSSEP.
A jawabinsa a lokacin kaddamawar da aka gudanar a yankin Ota shugaban karamar hukumar Ado-Odo/Ota Injiniya Sheriff Musa ya bayyana cewa, aikin na da mahimmancin gaske, musamman don amfanin alummar da ke a yankin
Musa ya kara da cewa, yana da kyau a yiwa dabbobin Allurar rigakfin da kuma samarwa da dabbobin Lasisi don a samar masu kariyar da ta dace, daga harbuwa da cutuka da sauransu
Shugaban ya kuma yaba da yin hadakar a tsakanin hukomin biyu, musamman don a kare lafiyar alumma da kuma ta dabbobin da ke a karamar hukumar.
A na sa jawabnin tun a farko, Daraktan kula da lafiyar dabbobi na ma’aikatar aikin noma da raya karkara Dakta Adeyemi Jolaoso ya sanar da cewa, ana samun karin cutukan da ke harbin dabbobi har a fadin duniya, inda ya kara da cewa, a saboda haka, yana da mahimanci a yi masu Allurar ta rigakafin a lunguna da sakuna na jihar.
Dakta Adeyemi wanda jami’in kula da lafiyar dabbobi na shiyya ya Dakta Tokunbo Oduloju ya wakilce shi a gurin kaddamawar ya ce, “Ana samun karin cutukan da ke harbin dabbobi har a fadin duniya, inda ya kara da cewa, a saboda haka, yana da mahimanci a yi masu Allurar ta rigakafin a lunguna da sakuna na jihar.”
Shi ma Likitan dabbobi na ma’aikatar aikin noma da raya karkara a jihar Dakta Aderounmu Ayopo ya bayyana cewa, shirin zai bayar da dama mai yawa wajen fadakar wa kan abinda ya shafi cutukan da ke harbin dabbobi.
Dakta Aderounmu ya kuma shawarci mazauna yankin su dinga tuntubar likitocin dabbo idan dabbobin sun kamu da wata cuta.
Wani mai kiwon dabbo kuwa Adewale Alani, ya nuna jin dadinsa ne kan Allurar rigakafin da aka yiwa dabbobin, inda ya bayar da shawar da a ci gaba da yin shirin na yiwa dabbobin Allurra rigakafin.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim