Gwamnatin Tarayya ta Saki Makudan Kudade don ciyar da yara yan Makaranta .
Gwamnatin tarayya ta ce ta fara fitar da kudade na zangon karatu na biyu na shirin ciyar da daliban makarantun firamari na kasa baki daya. Kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin LinkedIn mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar kula da al’amuran jin kai da ci gaban al’umma, Dr. Nasir Sani-Gwarzo.
Duk da cewa ba a bayyana adadin kudaden da aka za’a ba, Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa, kudaden zangon na farko na ciyarwa a shekarar 2023 ana fitar da su ne ga dillalan da gwamnatin kasar nan na Firamari
Ana sa ran za a yi amfani da asusun don samar da abinci kyauta ga ɗalibai 9,990,862 da ake ciyar da su a faɗin Najeriya.
Bada Abincin na da nufin haɓaka rajistar yara a makarantu da tallafawa musu da abinci mai gina jiki.
Gabanin Ziyarar Fafaroma, Wata Kasa A Afrika Ta Dakatar Da Tashin Jiragen Sama
An dakatar da tashin duk wani jirgin sama a Sudan ta Kudu gabanin ziyarar Fafaroma Francis a ranar Juma’a, inda hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta shaida wa kamfanonin jiragen sama cewa dole ne su soke ko kuma su dage ayyukansu har sai an dawo da jadawalin kamar yadda aka saba a ranar Litinin.
BBC ta ruwaito cewa, Fafaroma mai shekaru 86 a duniya ya kai ziyara sau da dama a Afirka tun bayan da ya zama Fafaroma a shekara ta 2013, amma wannan ita ce ziyararsa ta farko a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Sudan ta Kudu.