Karamin ministan albarkatun man fetur na ƙasa, Timipre Sylva ya ce daya daga cikin muhimman ayyukan ma’aikatar shi ne noman man fetur daga ganga biliyan 37 zuwa 40 nan da shekarar 2025.
Sylva ya bayyana haka ne a ranar Talata a wurin kaddamar da lasisin neman mai, mai lamba 809 da 810 a rijiyar kogin Kolmani II dake kan iyaka tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.”
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da shirin na Kolmani “Integrated Development Project” tare da wasu manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da gwamnoni da ‘yan majalisar ministoci da shugabannin masana’antu da jami’an kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) da dai sauran su duk sun hallara a yayin buɗe wannan wuri.”
Ƙaramin ministan Ya ce ya yi matuƙar farin ciki da haɗin gwiwar da aka yi tsakanin kamfanin NNPC, Sterling Global Oil, da Hukumar Bunkasa Cigaban Najeriya (NNDC), don gudanar da aikin hako man.
“Wannan shaida ce ta gaskiyar cewa har yanzu ɓangaren samar da makamashin lantarki na da alƙawarin dawowa kan zuba jari, yana mai nuna irin rawar da wannan albarkatun za ta cigaba da takawa wajen hada-hadar makamashin duniya,” in ji Sylva.
Ya tuna cewa a shekarar 2019 da NNPC ta bayyana cewa ta ci karo da man ‘kasuwanci’ a rijiyar kogin Kolmani II, al’ummar kasar sun yi bikin wannan labari a matsayin sakamako mai kyau na tsawon shekaru na binciken kasa.”
“Duk da ɗimbin ƙalubalen da NNPC ta fuskanta, ranar ta zo da za mu haɗa baki mu yi sheda tare da yin bikin haƙo ma’adinan ruwa a Arewacin kasar mu,” duk inji shi.
Sylva Ya ce ma’aikatar ta himmatu wajen nemo da samar da hanyoyin da za a kawo karshen talaucin makamashi, samar da wadata tare da dora al’umma mai dorewa.
Sylva ya ce Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA) ta ba da goyon baya da tsare-tsare don cimma wannan umarni ta hanyar samar da Asusun Haƙƙoƙin Man Fetur wanda NNPC za ta iya amfani da shi wajen tura fasahohin zamani na duniya don kawar da hatsaniya a cikin tudun mun tsira.
“Farkon hakar filayen Kolmani wanda zai iya ɗaukar gangar danyen mai da ya kai ganga biliyan ɗaya, zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa arzikin man fetur da kuma tabbatar da cigaba da wadatar makamashi,” inji shi.
Ya godewa shugaban ƙasa bisa nuna jajircewar sa na cigaban masana’antar man fetur ba tare da katsewa ba.
A nasa jawabin, babban jami’in kungiyar, NNPC, Malam Mele Kyari, ya ce an ƙara tantance mai da iskar gas a rijiyar mai na Kolmani a shekarar 2019 da kungiyar Kolmani ta tabbatar.
Kyari, yayin da yake miƙa godiyarsa ga gwamnatocin jihohin Bauchi da Gombe da sauran abokan huldar su, ya ce an samar da tsare-tsare don ba da tabbacin bayar da kudade da fasahar da ake bukata domin aiwatar da hadakar aikin.
Ya tabbatar wa shugaban ƙasar cewa za ta yi amfani da duk wani tsari da ya haɗa da tsarin samar da kuɗaɗe na ƙadarori don isar da aikin domin ya zama abin dogaro ga gwamnati.
Shugaban majalisar dattawan, Ahmed Lawan ya kuma yaba wa shugaban ƙasar bisa nasarar da ya samu, inda ya kara da cewa hukumar ta PIA a sashe na tara da biyar da hudu ta samar da kashi 30 cikin 100 na ribar hako man fetur.
Lawan ya ce nan ba da daɗewa ba jihohin Bauchi da Gombe za su ci gajiyar kashi 13 cikin 100 na abin da ake samu da kuma asusun cigaban al’umma wanda zai yi tasiri sosai ga rayuwar mazauna wurin.
Ya buƙaci gwamnati da ta yi amfani da kuɗaɗen shigar da ake samu daga man fetur don inganta rayuwar mazauna tare da tabbatar da tura fasahohi da kuma samar da muhalli mai inganci.
Shugaban majalisar dattawan, yayin da yake nuna rashin jin daɗinsa na ganin yankin Neja-Delter, musamman yankin Ogoni ya shawarci masu gudanar da rijiyoyin mai da su guji gurɓata muhalli.
A cikin jawabinsa, Manajan Daraktan kungiyar, NNDC, Shehu Mai-Borno, ya yi alkawarin ci gaba da kokarin ganin an samu ci gaba mai inganci.
Shima da yake jawabi, Manajan Darakta na Kamfanin Sterling Oil Exploration and Energy Production Company Ltd., Mista Mohit Barot, ya gabatar da wani gajeren faifan bidiyo da ke nuni da aikin.
Barot, yayin da yake gode wa Gwamnatin Tarayya bisa gano kamfanin a matsayin amintaccen abokin tarayya don cimma nasarar samar da makamashi, ya ce ya samu kudaden da ake bukata don aikin. (NAN)
Rahoto Fatima Nuraddeen Dutsin-ma.