Inganta harkar ilmi da kuma samar da kayan karatu na zamani a cikin manya da kananun makarantun mu wanda zai taimaka wajen mayar da Kasar mu Najeriya abin koyi a Nahiyar Afirka.
A wani rahoton kuma Atiku ya ƙara bayyana manufofinsa a yayin rantsar da gwamna Imole na jihara Osun.
Bikin rantsar da Sanata Ademola Adeleke ya wuce nasara ga mutanen jihar Osun.
Imole da ya fara haskawa a Osun a yau wata alama ce ta farfadowar kasar nan daga cikin duhun rashin shugabanci wanda za’a haɗu ayiwa ƙasa aiki tuƙuru.
Ɗan takaran Shugaban ƙasar a yana tsaka da bayyana manufofinsa sai ya ka da baki yake cewa, Tabbas Sai ya Tona Asirin Barayin Man Najeriya.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce daga yanzu ba za a samu maboyar barayin man fetur da abokan huldar su ba, komai girman daraja mutum a kasar nan, amma idan ya hau mulki a 2023.
Atiku ya yi wannan alƙawarin ne a ranar Asabar a Legas lokacin da yake tattaunawa da ɗimbin kamfanoni na Nijeriya a ƙarƙashin ƙungiyar masu ruwa da tsaki na Kasuwancin man.
Atiku ya kuma ce, domin ci gaban kasa, zai kwace duk wani man da aka ware wa wasu ‘yan Najeriya da suka gaza yin aiki.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar, wanda ya yi alkawarin ci gaba da yin mu’amala a kai a kai a tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwar kasar idan aka zabe shi a karagar mulki.
Ya kuma bayyana hanyoyin da zai tunkari abin da ya bayyana a matsayin tabarbarewar tattalin arziki.
Akan shirinsa na bunkasa fannin man fetur da iskar gas, Atiku ya bayyana cewa a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, an ware kason man da ake hakowa zuwa ganga miliyan hudu a kowace rana.
Wannan shirin, ya bayyana cewa, za a sake farfado da shi tare da dorewarsa fiye da adadin da aka zayyana, idan za a kada masa kuri’a a shekara mai zuwa, yana mai nuni da cewa domin yin hakan cikin nasara.
A wani labarin kuma: Kano: Yan APC Sun Bukaci A Hukunta Bashir Ahmad, Bayan Ya Halarci Qatar
Wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC, a Kano sun bukaci shugabannin jam’iyyar da su gaggauta daukar tsauraran matakai kan hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad.
Sun bukaci daukar matakin ne, bisa zargin rashin mutunta ci gaban jam’iyyar, inda ya tsallake tare da barin gangamin da jamiyyar ke yi, ta hanyar tafiyar Qatar, domin kallon gasar cin kofin duniya.