Haihuwana Na Farko Kenan”: Dattijuwa Yar Shekaru 54 Ta Haifi Yan Uku.
Allah ya albarkaci wata yar Najeriya da bata taba haihuwa ba da kyawawan yara har guda uku a lokaci daya
Dattijuwar mai shekaru 54 ta wallafa wani bidiyo a TikTok don nuna yadda ta yi goyon ciki da kuma haihuwar yaran
Tuni labarin haihuwarta a wannan shekaru ya yadu kuma ya ba mutane da dama a soshiyal midiya mamaki
Wata dattijuwa yar Najeriya na cikin yanayi na farin ciki yayin da Allah ya albarkaceta da samun haihuwar yan uku.
Bayan isowar kyawawan yaran duniya, matar mai suna @funmiedeni ta garzaya dandalin TikTok don nuna yadda ta yi goyon cikinta a bidiyo.
A bidiyon mai tsawon minti 1 da sakan 20, matar ta taka rawar farin ciki yayin da take baje kolin tulun cikinta a kaya daban-daban.
Baya ga hoton tulun cikinta, matar ta kuma nuna hotunan kyawawan yaranta yan uku.
A cewar matan, wannan shine haihuwanta na fari tana da shekaru 54. Hakan ya bai wa mutane da dama mamaki cewa ta dauki ciki a irin wannan shekarun.
Wadanda suka kalli bidiyon sun bayyana haihuwar yaran a matsayin mu’ujizar Ubangiji kuma sun yi addu’an samun irin haka.
“Ina rokawa abokiyar aikina irin wannan. Shekarunta 50 yanzu amma bata da haihuwa. Tana kula da yan biyu na kamar nata. Allah ya duba ki uwata.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim