Hukuma Ta Cafke Uba Da ‘Yayansa 2 Bisa Hada Kai Na Aika Wani Mutum Lahira A Yobe.
Yan Sanda Yobe Sun Kwamishe Wani Uba Da Yaransa Biyu Bisa Zargin Hada Karfi Da Karfe Wajan Aikata Laifin Kisa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta cafke wani mutum da ‘ya’yansa biyu kan zarginsu da hada karfi da karfe wajen kashe wani mutum mai suna Goni Waje a kauyen Dako Kangarwa da ke karamar hukumar Yunusari a jihar.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, ya bayar da sunayen wadanda ake zargi da suka hada da Jalomi, Ciroma da kuma Bulama.
Wa yan da ake zargin sun aikata wannan laifin ne domin buce takaicin su akan mamacin in da ya sha lugude a wajansu da jinkatawa.
A cewar sanarwar manema labarai da Kakakin ya fitar, ya ce, wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 7 ga watan Yuni, ya ce, ana zargin marigayin da rashin jituwa da mutumi da yaransa bayan wani lamari da ya shiga tsakaninsa da matar Bulama, karamin Chif wanda kuma mahaifi ne ga Jalomi da Ciroma
Ya kara da cewa, shaidun gani da ido sun yi bayanin cewa Alhaji Jalomi da Ciroma sun sassarawa mamacin da adda daga bisani suka banka masa wuta har ya mutu.
A yayin da suka banka masa wuta akwai wasu makwafta da suka hango lokacin da tuhumar ke afkuwa tsoron kar su zo taimakawa su ma a hada da su ya sa suka tsaya a nesa.
Yanzu haka wadanda ake zargin suna karkashin sashin binciken manyan laifuka kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban kotu.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim