Hukumar Hisba Ta Halasta Auren Matar Da Ta Kwace Saurayin Yarta A Kano.
Daga Nura Ahmad Hassan
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi watsi da ra’ayoyin da aka samu dangane da auren matar da ta auri tsohon mai neman auren ‘yarta a karamar hukumar Rano da ke jihar.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa matar mai suna Malama Khadija ta raba aurenta tare da auren saurayin diyarta.
Lamarin ya faru ne bayan diyar matar mai suna A’isha ta ki amincewa da mai neman nata, lamarin da ya haifar da cece-kuce a sakamakon haka hukumar Hisbah ta kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin.
Kwamitin da ya binciki ce-ce-ku-ce a kan auren ya mika rahotonsa da yammacin ranar Talata.
Da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin wanda ya zama mataimakin kwamanda mai kula da ayyuka na musamman na Hisbah, malam Hussain Ahmed, ya bayyana cewa kwamitin ya gano cewa auren ya dace kuma ya cika dukkan sharrudan da suka dace.
Ya bayyana cewa matar mai suna Khadija Rano, tsohon mijinta ne ya sake ta, kuma ta cika watanni uku (iddah) da Musulunci ya tsara, kuma daga baya ta auri wani mutum da diyarta ta rabu da shi a baya.
Ahmed ya yi watsi da rade-radin da ake yadawa cewa Khadijah tana ganin sabon mijin nata ta aure shi kuma ta ingiza mijinta ya sake ta domin ta auri mai neman diyarta.
Ya kuma bayyana cewa auren ya halasta bisa addinin Musulunci, inda ya ce dalilin da ya sa kwamandan Hisbah na karamar hukumar Rano ya goyi baya kuma halasta bikin auren.
Da yake mayar da martani babban kwamandan hukumar Hisbah Sheikh Harun Ibn Sina ya yabawa kwamitin bisa gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
Ya ci gaba da cewa, an zabo ‘yan kwamitin ne cikin tsanaki, saboda dimbin ilimin da suke da shi na koyarwar addinin Musulunci da fahimtar al’umma.
Ibn Sina ya ja kunnen jama’a da su guji yada labaran karya da kuma nisantar rashin fahimta kan al’amuran da suka shafi Musulunci.
Ya kuma shawarce su da su nemi ilimi, kasancewar Musulunci addini ne da ya kebe hukunce-hukuncen aure, da rayuwar iyali.