Tinubu Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Kungiyar IPOB Idan Ya Hau Mulkin Najeriya.
Ɗan takarar shugaban kasar jam’iyyar APC a Najeriya Bola Ahmed Tinubu yace idan ya lashe zabe mai zuwa zai tattauna da kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra da kuma irin ta dake sashen kudu maso gabashin kasar.
Tinubu ya ce ta hanyar tattaunawarce kawai za a saurari korafinsu da kuma zummar nazari akai ta hanyar warwaresu domin tabbatar da zama lafiya a Najeriya.
Dan takarar ya shaidawa magoya bayansa da ke jihar Imo cewar Najeriya na bukatar zaman lafiya saboda haka ya zama wajibi a gare shi da ya zauna da irin wadannan kungiyoyi domin ji daga wakilinsu kai tsaye.
Tsohon gwamnan Lagos ya kula alkawarin zuba jari mai karfi a bangaren Ilimi domin yaki da talaucin da ya addabi jama’a da kuma tabbatar da kawo sauyi ta hanyar da yara za su samu Ilimi.
Dangane da gudunmuwar da yankin kudu maso gabashin Najeriya ke bayarwa ta bangaren tattalin arziki kuwa Tinubu ya ce zai mayar da yankin kamar Taiwan da ke nahiyar Asia wadda ta yi fice a wannan bangaren.
Daga Abubakar Aleeyu Anache.