Ina Fatan Daura Ba Zata Muku Nisa Ba Bayan Mun Sauka Mulki, Buhari Ga Ministoci
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi bankwana da Minsitoci a taron FEC na karshe da ya jagoranta Ranar Laraba
Buhari ya fada musu kalamai masu ratsa zuciya, inda ya ce ya shirya karban duk wanda Daura ba ta masa nisa ba
A jawabin Buhari, ya ce bayan sauka daga mulki zai samu isasshen lokacin aiwatar da abubuwa da dama
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce a shirye yake ya karɓi bakuncin Ministocin ba basu hangi mahaifarsa, Daura, jihar Katsina da nisa ba bayan mulki ya kare ranar 29 ga watan Mayu.
Daily Trust ta ce shugaban ya bayyana haka ne a wurin taron majalisar zartarwa (FEC) na bankwana da ya gudana a fadar Aso Villa ranar Laraba.
Buhari ya ce bayan sauka daga mulki wanda ya shafe tsawon shekaru 8, zai samu isasshen lokacin da zai kula da Shanunsa da yake kiwo a Daura.
Shugaban kasa mai barin gado ya ce zai samu nutsuwa da farin ciki idan ya samu lokacin gudanar da wasu harkokin da hakan ba ta samu ba tun lokacin da ya shiga Ofis a watan Mayu, 2015.
“Ina kara gode wa Allah ya bamu kwarin guiwa kuma ya hada mu wuri daya zan tsumayi kowane daga cikinku, wanda Daura ba ta masa nisa ba domin ba zan dawwama a matsayin shugaban kasa ba.”
“Zan yi farin ciki idan na samu lokacin aiwatar da abubuwa da dama da ban samu damar yi ba tun ranar 29 ga watan Mayu, 2015. daya ciki shi ne kiwata garken shanu na.”
“Baki dayammu, ina mana fatan Alkairi da kuma fatan jin labari mai dadi a duk lokacin da aka ambaci sunayenmu. Muna kara godiya ga Allah tare da Addu’ar Allah ya albarkaci kasar mu Najeriya.”
Daga karshe, Muhammadu Buhari ya yaba da kwazon Ministocinnsa da kuma kokarin aiki tare da juna duk da kalubalen da suka fuskanta.
Ya kuma roke su da su goyi bayan gwamnatin zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda zai karbi ragamar mulki nan da ‘yan kwanaki.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim