Ina Son cigaba da karatu iyaye ba hali gashi mijin Aure ya ƙi zuwa – Ummulkhairi.
Wata Budurwa mai suna Ummulkhairi Ahmad, haifaffiyar garin Keffi Jihar Nasarawa, inda ta umarci da ALFIJIR HAUSA ta wallafa damuwarta ko Allah yasa a dace, musamma ga wanda zai iya ɗaukan nauyin karatunta.”
Matashiyar ta cigaba tsagewa ALFIJIR HAUSA cewa; ta Kammala matakin Sakandare tun a Shekarar 2016, amma babu labarin cigaba da kartunta, duba ga yadda iyayenta ba su da karfi, bisani ga fahimta Allah ya hore mata na karatu amma ba halin cigaba.”
“A don hakane take roƙon ga duk wanda Allah yasa yaji tausayinta da ya taimaketa ya ɗau nauyin karatunta zuwa mataki na gaba, bugu da ƙari ko mijin Aure tana SO.
Budurwar ta turowa ALFIJIR HAUSA sakon hakanne kai tsaye ta akwatin turo saƙonni don Jaridar ta bayyanawa Duniya irin halin da take ciki.
A ƙarshe dai matashi ta ajiyewa ALFIJIR HAUSA lamabar wayarta ga duk wanda Allah yasa zai taimaketa, zai iya tuntubarta kai tsaye don jiyo dukkan bayanai daga bakinta.
Layin akwatin tafi da gidanka ɗin na Ummulkhairi ɗin ya kama kamar haka ne; 08065785925.