Indiyawa maza 30 ne Suka yi Tattaki Domin Neman Matan da Zasu Auresu.
Wani matashi mai suna Mallesha DP ya ce mata kusan 30 ne suka ƙi amincewa da shi a cikin shekaru da suka gabata
A watan da ya gabata, wasu maza a jihar Karnataka da ke kudancin Indiya sun yi tattaki mai nisan kilomita 120 don ziyartar wani gidan ibada domin su yi addu’ar samun matan aure.
Hakan ya haifar da cecd kuce a yanar gizo, amma masu fafutukan sun ce hakan na nuni da zurfafa batutuwan zamantakewa da tattalin arziki a yankinsu.
Yawancin mazajen da suka fara wannan tattakin su 30, inda kuma yawansu ya kai 60 a dai dai lokacin da su ke gudanar da tattakin matasan sun kasance manoma daga gundumar Mandya ta Karnataka.
Mallesha DP ya ce Lokacin da ya kamata ya yi soyayya, baiyi ba sai ya shagaltu da aiki, ya samu kuɗi,” in ji shi. “Yanzu da ya mallaki komai na rayuwa, ya kasa samun yarinyar da zan aura.”
Mista Mallesha yana da shekaru 33 kacal, a halin yanzu amma ya ce duk in da yin tunanin cewa ya na son mace sai ace baza a bashi ba saboda yawan shekarunsa.
Shivaprasad KM, ya na ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya Tattakin, ya ce sama da mutane 200 ne suka sanya hannu don shiga cikin jerin masu tatakin a lokacin da suka fara sanar da ƙudirinsu.
ya ƙara da cewa mafiya yawan su sun koma gida saboda kafofin watsa labarai na cikin gida sun bayar da rahoton ta hanyar da ba ta dace ba,” in ji shi.
Wani daga cikin waɗanda suka shirya tattakin ya ce maza sama da 200 ne suka amince za su fito, amma sai suka ki fitowa daga bisani, bayan da kafofin yaɗa labaru suka bayar rahoton da ba na gaskiya kan su ba.
Mandya yanki ne da ke da albarka na filin gona saboda yawan manoma da yake da shi, in da suka fi yin noman rake. Sai dai raguwar kuɗaɗen da su ke samu d daga sayar da amfanin gona, ya sanya mutane ba sa marmarin auransu.
Mista Mallesha ya ce a cikin shekaru da suka wuce, kusan mata 30 ne suka ki shi, inda ya kwatanta sana’ar da yake yi da kuma rayuwa a karkara a matsayin dalilai da suka haddasa hakan.
Mista ya ƙara da cewa hakan ne ya sa su tattaki domin zuwa wurin bautan, domin sun san zai biya kudi buƙatar su
Masu fafutuka sun ɗora laifi kan halayen wasu magidanta da su ke hurewa ƴan matan kunne akan kar su aure masu noma domin noman rake ba zai riƙe su ba
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim