INEC ta bayyana dalilan da ya sa ƴan Nijeriya mazauna ƙasashen waje baza su iya zaɓe ba
2023: Shugaban INEC ya bayyana dalilin da yasa ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ba za su iya zaɓe ba.
Mista Yakubu ya ce INEC na goyon bayan kaɗa ƙuri’ar ‘yan Nigeria mazauna ƙasashen waje amma ya bayyana dalilin da yasa ba za’a bari ba a zaben shekaraar 2023.
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC), Mahmood Yakubu, a ranar Talata, ya bayyana dalilin da ya sa ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen ƙetare ba za su iya kaɗa kuri’a ba a zaɓen watan Fabrairun 2023 mai zuwa.
Da yake amsa tambaya game da jefa ƙuri’ar ƴan ƙasar waje a wani jawabi da aka yi a Chatham House da ke birnin Landan na ƙasar Birtaniya, ya ce duk da cewa hukumar zaɓe ta amince da hakan, amma dokar Najeriya ta sa ba za a iya kaɗa kuri’a irin wannan na ‘yan ƙasa a zaɓen ƙasar ba.
A baya gidajen jaridu sun buga cikakken jawabin Malam Yakubu wanda ya gabatar a lokacin zamansa a Chatham House.
Duk da haka, “Na gamsu da cewa lokaci ne kawai da za a cimma hakan,” in ji Mista Yakubu.
Ya bayyana cewa, hukumar na bin manufar buɗe kofa, kuma ta haɗa kai da ƙungiyoyi daban-daban har ta kai ga aikewa da ƙudurin zaɓen ‘yan ƙasashen waje zuwa majalisar dokokin ƙasar domin tattaunawa inda aka sha kaye.
Ƙoƙarin samun tsarin doka
Batun kaɗa kuri’a na ‘yan ƙasashen waje dai na zaman tattaunawa kuma yana daga cikin batutuwan da aka jefa domin tattaunawa a taron duba kundin tsarin mulkin ƙasar a bara.
A watan Maris na 2022, Majalisar Dokoki ta ƙasa ta yi fatali da ƙudurin zaɓen ‘yan ƙasashen waje ko da INEC ta ce ta shirya.
Hukumar ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NIDCOM) a watan Satumba na wannan shekarar ta ce za ta ci gaba da zage-zage.
Zaɓen ƴan ƙasashen waje na bai wa ƴan Najeriya da ba mazauna ƙasar damar zaɓe da kuma zaɓar wanda zai jagoranci ƙasar ta yammacin Afirka.
“Ya kamata a sasanta batun zaɓen waɗanda ke ƙasashen waje, kuma idan ka tambaye ni, zan ce kana yi wa waɗanda suka tuba wa’azi amma hukumar ba ta da hurumin tabbatar da hakan. Dole ne a samar da dokar da za ta iya faruwa,” Mista Yakubu ya lura.
Ya ƙara da cewa, “Ba wai kawai saboda kuɗaɗen da ake fitarwa ba kamar yadda mutane za su yi jayayya, amma saboda su ‘yan ƙasa ne kuma dole ne ‘yan kasa su sami ‘yanci,” in ji shi.
RAHOTO:- Comrade Yusha’u Garba Shanga.