Iska mai karfi ta janyo rasa rayukan Wasu Mutane Tare da lalata Wasu gidaje a Jigawa.
Mutane biyu ne aka tabbatar da rasuwarsu sakamakon wata mummunar iska mai ƙarfi da aka yi ranar Litinin a wasu sassa na jihar Jigawa
Shugaban Ƙaramar Hukumar Ringim, Shehu Sule-udi, ya ce iskar ta kuma bata gidaje guda 20 a kauyukan Larabawa da Hambarawa
Mutanen da lamarin ya rutsa da su sun yi kira zuwa ga gwamnati, masu hannu da shuni da sauran kungiyoyi da su zo su taimaka musu bisa wannan iftila’in da ya fada musu
Shugaban Ƙaramar Hukumar Ringim da ke jihar Jigawa, Shehu Sule-Udi, ya bayyana cewa akalla mutane biyu ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu a wata mummunar iska mai karfi da aka yi a yankin, ranar Litinin da ta gabata.
Mista Sule-Udi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a ofishinsa ranar Laraba, inda ya ce iskar ta kuma lalata gidaje akalla guda 20.
Shugaban ya bayyana yadda lamarin iskar ya faru ya ce an samu asarar rayukan na mutanen biyun ne a kauyukan Larabawa da Hambarawa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Ya ce lamarin ya faru ne da tsakiyar dare, wanda kuma ya janyowa mutane da dama rasa muhallansu.
Shugaban karamar hukumar ya bayyana lamarin a matsayin wani abu mara dadi, sannan ya yi alkawarin bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.
Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, a zantawarsu da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), sun yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su tallafa musu.
Aminu Hadi, daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, ta hanyar rasa gidansa da ya yi, ya bayyana lamarin a matsayin abu mai ban tsoro.
Hadi ya yi kira ga masu hannu da shuni, kungiyoyi da kuma gwamnati da su kawo musu dauki bisa iftila’in da ya fada musu, kamar yadda The Eagle Online ta wallafa.
Ya kuma yaba wa karamar hukumar bisa kawo musu dauki tare da bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim