Ɗaruruwan mutane ne suka fito kan tituna a manyan biranen ƙasar Sin a ranar Lahadin da ta gabata don nuna rashin amincewarsu da manufar ƙasar kan kullen Covid-19 zanga-zangar ya faru ne a wani yanayi da ba kasafai ke fitowa fili na nuna fushin jama’a a ƙasar.
Ƙwayar cutar a China tana tayar da hankalin jama’a, tare da gajiyawa da kulle-kullen, dogon keɓewa da kamfen ɗin gwaji.
Wata mummunar gobara da ta tashi a ranar Alhamis a Urumqi, hedkwatar lardin Xinjiang na arewa maso yammacin ƙasar Sin, ta zama wani sabon salo na nuna fushin jama’a, inda da yawa ake zargin dogon kulle-kullen Covid19 ya kawo cikas ga ayyukan ceto al’ummar.
Rahoto: Shamsu S Abubakar Mairiga.