Dakarun operation “forest sanity”sun kashe Yan ta’adda 2 a Kaduna.
Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da fatattakar wasu maboya a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, kamar yadda jami’an tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya bayyana.
Ya ce bisa ga bayanan aiki da gwamnatin jihar ta samu, sojojin sun samu nasarar ne a lokacin da suke sintiri a dajin Kaboresha-Rijana-Kuzo-Kujeni-Gwanto-Kachia.
“Sojojin sun yi kwanton bauna a kan hanyar Gwanto zuwa Kwasau, inda suka yi artabu da ‘yan bindiga da suka nufo wurin a kan babura. Sojojin sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da kwato babura uku.
“Sojojin sun kuma kai farmaki kan sansanonin ‘yan bindiga a yankin Kutura-Rijana. ‘Yan bindigar sun tsere zuwa cikin dajin da ganin sojojin, inda suka lalata sansanonin tare da kwato babura uku.
“Sauran abubuwan da aka gano sun hada da kakin sojoji da dama da kuma na bandoli.
“Ana ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda kuma gwamnati ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da sa kai ga bayanai masu amfani,” in ji shi.
A cewar sanarwar, gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana gamsuwarsa tare da yaba wa sojojin bisa kokarin da suka yi wanda ya haifar da nasara a baya-bayan nan.
RAHOTO -ALIYU SHU’AIBU ALIYU (MARIRI)