“A jiya Asabar da misalin ƙarfe takwas na safe, Jami’an tsaro sukayiwa dajin ƙaramar hukumar Ɗan-musan kawanya. “inda Wakilanmu ke shaida mana cewa, an samu Nasarar bindige Ƴan ta’adda tare da ƙone sansaninsu baki ɗaya.”
“Wakilin ALFIJIR HAUSA ya zanta da wani mazaunin yankin, wanda ya shaida masa cewa, a jiyan bayan shigar jami’an tsaron sojojin Nijeriya cikin dajin, suka sanya dokar hana zirga-zirgan al’umma da nufin daƙile tserewar Ƴan bindigan a lokacin da suka ji narko na Ruwan bama-bamai daga dajin.”
Bugu da ƙari sai dai shi mazaunin yankin a yayin Zantawarsa da wakilinmu na Jaridar ALFIJIR HAUSA tare da mal. Zaharaddeen Sani Dutsin-ma ya ƙara da cewa, akwai wasu hanyoyi da aka yi shekara goma cif-cif ba’abin su saboda yadda ɓarayin daji suka addabi Hanyar.
“Har wala yanzu, a cigaba da zantawar wakilinmu da shi mazaunin ƙaramar hukumar Ɗan-musan, ya ce a jiya Asabar ɗin yankunan sun cigaba da Safarar kayan masarufin cikin kwanciyar hankali suna fitowa da shi cikin gari suna cinikayya a bisa kan bauransu.”
“Hakazalika al’ummar wannan yankin sunata godiya ga jami’an tsaron sojojin Nijeriya da suka yi wannan hoɓɓasan na kawo masu ƙarshen Ƴan ta’addan da suka addabesu.”
“Al’ummar ƙaramar hukumar Ɗan-musan sun yi ta farin ciki da muna godiyarsu ga jami’an tsaron sojojin Nijeriya bisa irin bajintar da suka yi na kashe Ƴan bindigan dajin ta hanyar ƙona su da wuta.”
“ALFIJIR HAUSA ta cigaba da bin diddigin lamarin, inda ta ƙara samun tabbacin cewa an samu wannan gagarumin murƙushe sansanin Ƴan ta’addan daga bakunan Al’umma.”
“A halin yanzu dai yankunan ƙaramar hukumar Dutsin-Ma, abinda ya haɗa da Safana, Ɗan Musa, cikin taimakon Allah da jajircewar jami’an tsaron an samu sauƙin hare-haren Ƴan ta’adda.”
Jami’an tsaron mazauna ƙaramar hukumar Ɗan-musan, sun bada sanarwar cewa al’umma su cigaba da taya su aiki tuƙuru ta hanayar saka idanu ga duk wani abu da suka gani wanda zai zama barazana ga rayuwarsu.”
“A jiya Asabar dai al’umma suka riƙa shewa da nuna farin cikinsu kan wannan babban Nasara da aka yi kan Ƴan ta’addan daji.”
Wakilinmu Mal. Zaharaddeen Sani Dutsin-ma, ya cigaba da bibiyar al’umma duk a jiya Asabar ɗin a domin jiyo ta bakinsu kan wanann babban Nasara da akayi, bisani kuma an samu kyawawan kalamai daga bakunan al’umma tare da yiwa Allah (S.W.A) godiya.”
“Sai dai wani hanzari ba gudu ba, al’umma mazauna duk yankunan da al’amarin Ƴan ta’addan ke addabarsu na Yankunan jihar Katsina suna cigaba da zaman kare kai kamar yadda gwamar jihar Katsina ɗin Aminu Bello Masari ya umarta al’umma da su tashi kai tsaye haiƙan a domin kare kansu.”
Bayan haka kuma mun samu tabbacin hakan yadda al’umma musamman yankin ƙaramar hukumar Dutsin-Ma ke ta azama ana zaman kare kai daga miyagu ɓarayin daji.
“Idan mai Karatu bai mantaba duk dai a jiya Asabar ɗin jaridar ALFIJIR HAUSA ta Ruwaito cewa, manoma a ƙaramar hukumar Dutsin-Ma suna cigaba da girbe amfanin gonarsu daga wurare mafiya hatsari na matsalar tsaro, wanda a can baya wurin ba ya biyuwa bare har ayi noma.”
“A cigaba duk dai a cikin kanun labaran namu dajin da Jami’an tsaron sukayi raga-raga da shi a ƙaramar hukumar Ɗan-musan yana nan a ƙone babu ko wani mahaluƙi da yayi saura da rai biyo bayan wannan farmaki da jami’an tsaro suka, kai komai na cikin dajin ya tashi aiki.”
Daga Zaharadden Sani Dutsin-ma.