Jam’iyyar APC za ta sake farfadowa a jihar Kano – Gwamna Ganduje yasha alwashi.
Gwamna Ganduje ya ce jam’iyyar za ta bar madafun ikon jihar ne kawai na wasu dan gajeran lokaci kafin ta sake dawowa
Ganduje ya ce tarihi zai maimaita kansa na abinda aka taba yi wa tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta All Progressive Congress (APC), za ta bar jihar Kano ne kawai na wani dan lokaci, kafin ta sake dawowa.
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa Ganduje, ya yi wannan furucin ne wajen ƙaddamar da sabuwar hanyar da aka yi a Kwanar Dala, cikin ƙaramar hukumar Dala ta jihar, a yammacin ranar Litinin.
Gwamna Ganduje ya kuma nemi yafiyar al’ummar jihar wadanda ya batawa rai a lokacin da ya kwashe kan madafun ikon jihar, cewar rahoton The Guardian.
“Wannan hanyar aikinta ya kammala sannan gashi yanzu mun taro anan domin kaddamar da ita. Wannan kaddamarwar mun yi mata laƙabin ta bankwana, saboda tana ɗaya daga cikin ayyukan karshe da za mu kaddamar domin yi wa al’ummar Kano bankwana, amma na dan gajeran lokaci.”
Ganduje ya ce tarihi zai maimaita kansa dangane da Dawo-Dawo, (shahararriyar wakar da aka yi wa sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin ya dawo ya sake mulkar jihar, bayan mulkinsa na farko).
A cewarsa ko Dawo-Dawo da aka yi a baya, mu ne mu ka tsaya tsayin daka ta tabbata, saboda haka yanzu kada mu manta da wakar dawo-dawo.”
Ganduje ya kuma kaddamar da wasu hanyoyin guda uku da suka hada da hanyar Bello Kano, hanyar Kwanar Dala da wata kuma a Babban Layi Kurnar Asabe, cikin karamar hukumar Dala ta jihar.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.