Kimanin kungiyoyin sha biyu ne daga gidan ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alh Atiku Abubakar suka sauya sheƙa a jiya zuwa jam’iyyar APC ƙarƙashin Alh Mas’ud Ɗan Group.
Yayin sauya sheƙar ta su, gwamnan jihar Zamfara Matawallen Maradun kuma shugaban kamfen din Tinubu na shiyyar Arewa maso yamma shine ya karɓi sauya sheƙar ta su a jihar Kaduna.
Alh Abdallah Abdulkarim Gama wanda shine shugaban kungiyar nan ta Tinubu Arewa Reporters ya shaida mana cewa wannan shine lokacin da suka fara zabarin duk wani mai muhimmanci kama daga Kungiyoyi zuwa ɗaiɗaikun mutane daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC don tabbatar da nasarar Tinubu/Shettima a zaben 2023.
Matasan sun bayyana goyan bayansu 100% ga jam’iyyar APC kuma sunyi alkawarin ba da tasu gudummawar don tabbatar da nasarar APC, haka zalika dukkan wani aiki da da kungiyar ta Tinubu Arewa Reporters take yi a yanzu tana yin su ne karkashin sakataren ta Alh Shehu Dabai.
Daga Comrd Haidar Hasheem Kano