Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sadaukar da wani buri na ƙashin kansa domin cigaban ƙasa, kuma yana samun nasarar lashe zukatan ‘yan Najeriya da ma duniya a matsayinsa na mai son zaman lafiya, ta hanyar cigaba da zaman lafiya da kuma burinsa a kasashe da dama.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a cikin sakon da ya aike a madadin gwamnati da kuma ‘yan Najeriya na bikin cika shekaru 65 na tsohon shugaban kasar a ranar Asabar.
A cewar wata sanarwa da Femi Adesina, mai baiwa shugaban jasa shawara kan Harkan yaɗa labarai ya fitar, shugaba Buhari ya lura da matsayinsa na tsohon shugaban kasar wajen cigaban kasa da cigaban kasa.
Shugaban ya bayyana imanin cewa abokantaka, aminci, da kuma tawali’u na Dr Jonathan ya ci gaba da buɗe damar yin hidima ga bil’adama tare da bayyana hanyar da tsohon shugaban kasar zai iya saka hannun jari a cikin mutane, cibiyoyi, da kasashe.
Yayin da Dr Jonathan ya cika shekaru 65, shugaba Buhari ya yi addu’ar fatan alheri da kuma iyalansa.
Tsohon shugaban kasar ya nuna farin cikinsa ƙwarai, ganin yadda shugaba Muhammadu Buhari ke masa irin wannan yabo tare da jinjina masa kan irin namijin ƙoƙarin da ya yi lokacin yana shugaba ƙasar Nijeriya.”