Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya shaidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya cire shi cikin gwamnonin da ake kyautata zaton suna wawushe kudaden da aka ware wa kananan hukumomin jihar.
A cewarsa gwamnatin jihar na tallafa wa kananan Hukumomin jihar da naira miliyan 300 duk wata domin su samu damar biyan albashi.
Da yake mayar da martani a garin Asaba ta bakin babban sakataren yada labaransa, Olisa Ifeajika, Okowa, wanda shine mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya ce abin takaici ne yadda shugaban ya yi irin wannan magana.
Shugaban ya yi ikirarin cewa gwamnonin na yin kutse a kan kudaden da ake ba kananan hukumomi duk wata.
A cewar Mista Ifaejika, alkawurran da gwamnan ke yi a kan kananan hukumomi ba su da misaltuwa.
“Yana yin wannan a addinance. Ga mai yin haka, ta yaya zai kasance cikin masu satar kudin Karamar Hukuma?
Gwamnan mu ba ya cikin sa, ko da za’a lissafo gwamnonin da suka kasance a wancan bangaren da shugaban ke magana, tabbas Okowa ba zai kasance a wurin ba.
“Zai kasance cikin wadanda za’a rubuta sunayensu da zinare saboda yin adalci da daukaka ga kananan Hukumomin a jihar Delta.
“Kuna sane da yadda gwamnatin jihar ta bayar da Naira biliyan 5 wanda daga cikin Naira biliyan 2.5 na tallafi ga wadanda sukayi ritaya, da sauran su.
Yana tabbatar da cewa JAAC na taruwa akai-akai don tabbatar da cewa abubuwa sun tafi daidai.”
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida.