Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar wazirin Adamawa ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya caccaki ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, kan kalaman da ya yi ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ɗin Atiku Abubakar.
Tinubu, a lokacin da yake jawabi a Warri a wajen kaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar Delta na jam’iyyar APC a ƙarshen mako, ya nuna shakku kan bayanan Atiku, inda ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya fito fili ya yi faɗa da shugaban sa, Olusegun Obasanjo.
Suna gaya mana yadda suka kashe kuɗin PTF don siyan motoci ga matansu na sharholiya Suna da kunya? Tinubu ya tambayi jama’ar garin Warri.
Kakakin kwamitin yaƙin neman zaben PDP, Sanata Dino Melaye, a wata sanarwa da ya sanya hannu, ya bayyana tsohon gwamnan Legas a matsayin maci amana da bai kamata a amince da shi ba.
Sanarwar ta cigaba da cewa, “A cikin wani yanayi na wucin gadi, Ahmed Bola Tinubu, mai rike da tutar jam’iyyar APC, a jihar Delta, kamar yadda ya saba ya bar al’amura tare da mayar da hankalinsa kan mai girma Atiku Abubakar, wanda ya zama dole. Saboda An yi masa mafarki mai ban tsoro game da zaɓen shugaban kasa na 2023, yadda PDP za ta yi biji-biji da shi.
“A cewar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Atiku ya ‘yaƙi’ Obasanjo a lokacin da yake mulki.
Al’umma Werri Sun ce Suuna godiya matuƙa da yadda Tinubu ya tuno da wannan kyakkyawar ɗabi’a ta Atiku Abubakar, wanda a lokacin da yake riƙe da muƙamin mataimakin shugaban ƙasa a Tarayyar Najeriya ya kare ƙundin tsarin mulki da zurfafa dimokaraɗiyyar Najeriya.
Haka zalika Ba abin mamaki ba ne Tinubu zai jefar da mutumin da ya karya doka, duk a cewar maosyansa.”
Mutumin da ke neman bin doka ta fuskoki da dama ba zai iya ganin cancantar kare doka ba Tunubu ya cigaba da caccakar Atiku Abubakar.
Kakakin Yaƙin Neman zaɓen Atiku Malaye yayin maida martani ya ƙara da cewa, Babu shakka wannan matsayi zai sha bamban da na mutum azzalumi magabata irin su Tinubu, wanda a baje kolin ra’ayin demokraɗiyya ya fafata da mataimakiyar gwamnansa mata, Misis Kofo Akereke-Bucknor, har sai da aka tsige ta daga mukaminta.
A cigaba kakakin yaƙin neman zaɓen ya ce “kore mataimakin gwamnan na farko Tinubu daga mukaminsa babban cin amana ne ga kungiyar Afenifere, wadda ta zabi tsohon mataimakin gwamnan a matsayin wani bangare na fahimtar ƙungiyar na goyon bayan zaɓen Tinubu a matsayin gwamnan jihar Legas.
Wannan hali ya nuna cewa ba za’a iya amincewa da Tinubu da mulki ba, duk inji kakan yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ɗin.
Daga Salma Ibrahim Ɗan-ma’azu.