Karancin man fetur zai shude a mako mai zuwa, Kyari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya.
Babban Jami’in Kamfanin Mai na Najeriya Mele Kyari, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a samu saukin matsalar karancin man fetur a mako mai zuwa.
Kyari ya bayyana haka ne a wani shirin bidiyo da aka nuna a gidan talabijin na Channels a yammacin ranar Talata.
Sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da cewa layukan gidajen man za su bace ba, amma ya kara da cewa za a samu ci gaba sosai nan da mako guda.
Ya ce, “Yanzu nan da mako guda mai zuwa, ba ina nufin baza ku samu jerin gwano nan da mako guda ba, a’a, domin abubuwa da dama sun fita daga hannunmu, kuma ba shakka ‘yan kasuwar sun yi kasa a gwiwa.
“Amma na yi imanin cewa za mu ga sauƙi mai ma’ana idan aka kwatanta da yau a cikin mako guda mai zuwa.
“Ina neman afuwar lamarin a madadin mu duka a masana’antar mai da iskar gas.”
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa karancin man fetur tare da karancin sabbin takardun kudi na naira da kuma tsofaffin kudade sun jawo wa ‘yan kasa wahalhalu da gurgunta harkokin tattalin arziki a fadin kasar.
Sakamakon haka zanga-zanga ta barke a jihohi da garuruwa daban-daban a fadin tarayyar kasar, inda ‘yan kasar suka koka kan karancin tagwayen da kuma illar kasuwancinsu da na yau da kullum.
Idan dai za a iya tunawa, Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya kuma bukaci ‘yan Najeriya a makon jiya Juma’a da su ba shi kwanaki bakwai daga nan don magance matsalar Naira, saura kwana biyu a cika kwanaki bakwai da shugaban ya bukata. .
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida