Hon Sani Sha’aban, na daya daga cikin wadanda suka nemi takarar gwamna a APC a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya, ya ce ya bar jam’iyyar tasu ne saboda kaucewa manufofin da aka kafata.
Ya ce, kowa ya san manufofin jam’iyyar APC, shi ne tabbatar da gaskiya da adalci.
Hon Sani Sha’aban, ya ce,” Duk wanda yake siyasa ba ma wanda ke jihar Kaduna ba, in dai ya san menene siyasa, to ya san cewa ba haka yakamata ayi ta a jihar Kaduna ba.”
Ya ce,” A tsarin doka an san cewa deliget ne ke zabar ‘yan Takara, to mu a jihar Kaduna akwai wanda ya ga an yi zaben deliget?
Hon Sani Sha’aban, ya ce da ace deliget ne suka yi zaben ‘yan takara don ace ya fadi takara ba zai damu ba don ya san kaddara, to amma ba a yi ba.
Ba ya ga zargin rashin adalcin da ya ce an yi masa, ya ce tuni ya yi nisa wajen tattaunawa da wasu jam’iyyu da nufin tsayawa takarar gwamnan jihar ta Kaduna a zaben da ke tafe.
Ya ce, ya yanke hukuncin komawa wata jam’iyya don tsayawa takara ce saboda kundin zaben 2022, ya bayar da damar kowacce jam’iyya tana da damar canja dan takarar gwamna har zuwa 12 ga watan Disambar 2022.
Ya ce,’’ Don haka a yanzu ni ina damar da zan koma wata jam’iyya na tsaya takarar gwamna don akwai sauran lokaci kafin cikar wa’adin.”
Tuni dai wasu shugabannin jam’iyyar ta APC, suka yi watsi da zarge-zargen cewa jam’iyyar ta aikata rashin adalci.
Hon Yahaya Baba Fate, shi ne sakataren jam’iyyar APC rashen jihar ta Kaduna, ya shaida wa BBC cewa, ba bu wata jam’iyyar da zata so ta rasa da ko da guda, to amma maganar rashin adalcin da wasu ke yi wa jam’iyyar ba haka bane.
Ya ce,” Shi wanda ke cewa jam’iyyar bata adalci wajen bawa kowa dama, ai da ba a bashi takara ba.”
Hon Yahaya Baba Fate, ya ce su a matsayinsu na shugabannin jam’iyya basu san wata gudunmuwa da Hon Sani Sha’aban ya bawa jam’iyya ba, amma duk da haka aka bashi takarar.
To amma ba mamaki babban dalilin fitarsa daga APC, zafin kayi ne, inji shi.
Batun sauya sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan, kusan wani lamari ne Daya zama tamkar ruwan dare a Najeriya.