Ko Ban Faɗa Ba Na San ‘Yan Najeriya APC Za Su Zaɓa A 2023 – Gwamna Ganduje ya bayyana.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yace tsarin karba karba shine yafi dacewa da kasar nan a wannan lokacin.
Ganduje ya bayyana hakan ne a yammacin yau Juma’a yayin zagayen yakin neman zabe da kuma tuntuba na Dan takarar gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakin sa Murtala Sule Garo wanda ya gudana a yankin Dambatta da Makoda.
Yace tsarin siyasar bana cike yake da inganci, inda ake yin komai a fayyace yadda al’umma zasu gane wadanda ya Kamata su zaba a matsayin wakilan su a matakai da ban da ban.
Yana mai cewa lokacin yayi da za’a gwada Dan takarar da ya fito daga kudancin kasar nan wato Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Gwamna Ganduje ya Kara da cewa Yana da yakinin al’ummar Makoda da Dambatta baza su ki amincewa da salon karba karba ba.
A nasa jawabin mataimakin gwamnan Kano Kuma Dan takarar gwamna Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana cewa lokaci yayi da mutanen yankin zasu saka alherin da gwamnati ta dade tana yi musu ta fuskar Samar da ayyukan raya yankin na Dambatta da Makoda, inda ya bayyana gamsuwa da tarbar da suka samu.
Ya kuma nemi goyon baya da hadin kan jama’a a ranar zaben dake karatowa, wajen dangwala musu.
Taron dai ya samu halartar manya da kananan ‘ya’yan jam’iyyar APC na Jihar Kano.